1) Kafin ka yi aure dole ka samu cikakken sani game da aure, ฦa'idoji da sharuษษan da Allah (s w a) ya shimfiษa a cikinsa 2) Kafin ka yi aure yรฃ dรฃce ka samu ilimin yadda zรฃ ka mu'amalanci matarka gurin mu'amalar aure, don gudun faษawa cikin jagwalgwalo 3) Dole ka san cewa kaine wanda Allah ya ษorawa alhakin ciyar da iyalinka, ilmantar da su, tufatar da su da nema musu lafiya lokacin da suke cikin rashin lafiya 4) Ya zama dole ka samu cikakkiyar sana'ar da zaka iya ษaukar duk wata ษawainiyar iyalanka kafin kayi aure. Addini ma bai yarda wanda ba zai iya ษaukar nauyin iyali ya yi aure ba 5) Idan kana son ษorewar zaman aurenka, to sai ka samu kyakkyawar niyya game da auren, ba don sha'awa kawai ko dan abokanka sun yi aure kaima za ka yi ba 6) Ya dace ka bayyanawa wadda zaka aura ainahin ษabi'unka, kar ka ษoyewa wadda zaka aura ษabi'arka, idan ษabi'ar mara kyau ce, sai kayi ฦoฦarin gyarawa 7) Kada ka nunawa wadda zaka aura kai mai wadata ne alhalin ba ...
Comments
Post a Comment